O.J Simpson Ya Rasu

SIMPSON

OJ Simpson ya kasance 76

WASHINGTON, D. C. - O.J. Simpson, tsohon babban ‘dan wasan kwallon kafa na Amurka wanda aka zarge shi kuma a karshe aka wanke shi daga kisan gillar da aka yi wa tsohuwar matarsa da kawarta a 1994, ya rasu, a cewar danginsa. Ya kasance 76.

Obit OJ Simpson

Obit OJ Simpson

"A ranar 10 ga Afrilu, mahaifinmu, Orenthal James Simpson, ya rasu a yakinsa da ciwon daji, 'ya'yansa da jikokinsa a lokacin suna kewaye da shi. A wannan lokaci na wannan babban rashi, iyalinsa sun nemi da a girmama bukatunsu na sirri da alheri, ", kamar yadda sanarwa da iyalansa su ka fitar ta bayyana.