PDP Na Daukar Matakan Kwace Madafun Iko A Najeriya

Sanata Ali Modu Sheriff

Yayin da gwamnatin Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ke cika shekara guda a watan mayu na gobe, Jam’iyyar Hamayya ta PDP tana daukar matakan kwace madafun iko a shekara ta 2019. Hakan dai na daga cikin kalaman shugaban PDP na kasa Sanata Ali Modu Sheriff lokacin daya ke jawabi ga ‘yayan Jam’iyyar jiya a Dutse jihar Jiagwa.

Shugaban wanda ya fara da jihar Jigawa a jadawalin kewaya jahohin Najeriya da ya tsara, domin ganawa da magoya baya gabanin taron kolin jam’iyyar ta PDP da za a yi a watan gobe, yace hakan na daga cikin alkawarinsa na farfado da ruhin jam’iyyar.

Shi kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, dake zaman babban mai masaukin baki ya yi jawabi a taron inda ya furta kalaman da ke koda sabon shugaban Jam’iyyar Ali Modu, yayi kuma fatan sake karbar ikon jihar a zaben shekara ta 2019.

Dangane da tsarin yar tinke da PDP tace zatayi amfani da shi wajen fitar da yan takara a zaben 2019, Ambasada Kazaure yace, yin hakan zai nunawa Najeriya cewa Dimokaradiyya ta nuna a wajen yan PDP, haka kuma za a gudanar da hakan ba tare da samun tangarda ba, harma da zaben wanda jama’a ke so.

Saurari rahotan don karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

PDP Na Daukar Matakan Kwace Madafun Iko A Najeriya - 2'57"