PDP Mai Mulkin Najeriya Na Kara Fama da B'araka

wani mai goyon bayan jam'iyar PDP ya na rike hula mai laima

Rikicin jam'iyar PDP mai mulkin Najeriya na dada ta'azzara a lokacin da ake kokarin yin sulhu da daidaita tsakani
Kamar yadda masu hikimar magana ke cewa ana magani kai na k'aba, al'amarin jam'iyar PDP mai mulkin Najeriya sai kara tabarbarewa yake yi a yayin da baraka ke dada yin fadi tsakanin masu yin mubayi'a ga Bamanga Tukur ko Abubakar Kawu Baraje. Duka wannan kuwa na faruwa ne a daidai lokacin da masu sauran kwarin guiwa a jam'iyar ta PDP ke ci gaba da kumajin neman dinke baraka da sasanta tsakani, kamar yadda za ku ji a cikin wannan rahoto d Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko ma na daga Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Rikicin PDP na dada karuwa - 1:56