Accessibility links

Shugabannin PDP Tsohuwa Sun Ce Za A Dinke Baraka


Wani taron jam'iyyar PDP mai mulki a Nijeriya. Akan auna tarurrukan siyasa da bama-bamai a Nijeriya a 'yan kwanakin nan.

Amma 'yan santsin PDP sun ce, tuni ma jama'a talakawa suka bar PDP din, masu ci a jikin gwamnati kadai suka rage cikinta

Yayin da shugabannin bangaren bamanga Tukur na jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya suke nuna kwarin guiwar cewa jam'iyyar zata komo ta sake hadewa cikin lumana, wasu 'ya'yanta dake ganin an nuna musu rashin adalci sun ce a kai kasuwa.

Shugaban majalisar amintattun jam'iyyar ta PDP, Tony Anenih, yana cikin wadanda ke ganin cewa 'ya'yan jam'iyyar da suka yi tawaye suka balle, zasu komo a sasanta da su, su kuma bayar da gudumawa ga nasarar jam'iyyar a nan gaba.

Amma da yawa daga cikin wadanda suka balle daga jam'iyyar, sun ce tun ma kafin su balle daga cikinta, talakawan Najeriya sun yi watsi da ita, sauran mutanen dake samun wani abu a wurin gwamnati kawai suka rage cikinta, su din ma domin abinda suke samu din ne ba wai domin cewar jam'iyyar ta dace da ra'ayoyinsu ba.

Wakilin Muryar Amurka, nasiru Adamu el-Hikaya, ya hada mana rahoto na musamman a kan wannan...

XS
SM
MD
LG