PDP ta tura mukamin dan takarar shugaban kasa arewa a zaben 2019

Sanata Ali Modu Sheriff shugaban jam'iyyar PDP

Jam'iyyar PDP ta amince zata tura mukamin dan takarar shugaban kasa zuwa arewa a zaben 2019 idan Allah ya kaimu har da ma na shugaban jam'iyyar

Wannan matakin da jam'iyyar ta dauka ta bata alama ce cewa shugaban jam'iyyar na yanzu Ali Modu Sheriff dake karkare wa'adin Adamu Mu'azu zai iya cigaba da zama shugaban jam'iyyar har zuwa shekarar 2019.

Wasu sun fara rade-radin wai Ali Modu Sheriff din ka iya samun damar tsayawa takarar shugaban kasa. Matsayin jam'iyyar ya kawo muradun wasu dake son kawo karshen shugabancin Modu Sherrif.

Shi ma kakakin PDPn Oliseh Metuh dake fuskantar badakalar cin hancin nera miliyan dari hudu yace ba zai tsaya takarar neman kowane mukami.

Sakataren amintattun PDP Alwalid Jibril yace duk binciken da EFCC zata yi ba zai shafi irinsa ba saboda bai yi awan gaba da ko kwandala ta barauniyar hanya ba. Yace shi kudinsa yake kashewa.

Shugaban EFCC Magu yace zasu cigaba da ayyukansu ba sani ba sabo.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

PDP ta tura mukamin dan takarar shugaban kasa arewa a zaben 2019 - 2' 59"