Qatar 2022: Ghana Ta Doke Koriya ta Kudu Da Ci 3-2 Bayan Zazzafar Karawa

'Yan wasan Ghana suna murnar lashe wasansu da Koriya ta Kudu

Ghana dai ta gaza cin wasanta na farko da Portugal a farkon bude gasar wacce ake yi a Qatar.

Tawagar ‘yan wasan kasar Ghana ta kaucewa ficewa daga gasar cin kofin duniya bayan da ta doke Koriya ta Kudu da ci 3-2.

Dan wasan Ghana Mohammed Salisu ya zura kwallaye biyu sannan Muhammad Kudus shi ma ya ci kwallo daya.

Wannan wasa dai ya yi zafi tsakanin bangarorin biyu wadanda suka yi ta kai wa juna hare-hare musamman bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Ghana dai ta gaza cin wasanta na farko da Portugal a farkon bude gasar wacce ake yi a Qatar.

Dan wasan Koriya ta Kudu, Cho Geu-sung- Cho ne ya ci wa Koriyar kwallayenta biyu bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Ghana ce ta fara cin kwallayen biyu na farko inda wasa ya kai 2-0, sai dai Sung ya farke duka kwallayen, kafin daga bisani Kudus ya kara kwallo ta uku a ragar Koriya ta Kudu.