Quarterfinls: Gasar Zakarun Turai A Wannan Mako

Kofin Champions League

Karawar da za ta fi daukan hankali za a yi ne tsakanin Real Madrid da Manchester City mai rike da kofin a ranar Talata inda City za ta bi Madrid Santiago Barnebeu.

A wannan mako za a dawo karawa a gasar Zakarun Nahiyar Turai ta UEFA Champions League a matakin Quarterfinals.

Karawar da za ta fi daukan hankali za a yi ne tsakanin Real Madrid da Manchester City mai rike da kofin a ranar Talata inda City za ta bi Madrid Santiago Barnebeu.

Wata karawa da ita ma za ta dauki hankali ita ce tsakanin Arsenal da Bayern Munich inda Bayern za ta bi Arsenal filin Emirates.

A ranar Laraba kuma 10 ga watan Afrilu PSG za ta bi Barcleona gida yayin da ita kuma Burrsia Dortmund za ta bi Atletico gida.

Wadannan wasannin za a yi su ne a matakin zagayen farko inda kungiyoyin da suka karbi bakunci su ma za su bi wadanda suka karba gida.