Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Ta Fara Hangen Kofin Champions League Na 15


'Yan wasan Real Madrid lokacin da suke murnar zura kwallo a ragar Chelsea
'Yan wasan Real Madrid lokacin da suke murnar zura kwallo a ragar Chelsea

Madrid, wacce ita ke rike da kofin gasar, ta bi Chelsea har gida ta doke ta, abin da ya ba ta damar shiga zagayen semi-finals.

Real Madrid ta fara jin kamshin kofin gasar kofin Zakarun Nahiyar Turai na Champions League bayan da ta lallasa Chelsea da ci 2-0.

Rodrygo ne ya ci duka kwallayen.

Madrid, wacce ita ke rike da kofin gasar, ta bi Chelsea har gida ta doke ta, abin da ya ba ta damar shiga zagayen semi-finals.

Sai dai da a ce Chelsea ta yi amfani da damammakin da ta samu, da ta ba Madrid wahala matuka musamman a bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

N’Golo Kante ya zubar da wasu damammaki tun kafin a fara zura kwallaye a wasan.

Sau 14 Madrid ta lashe kofin gasar ta UEFA, yayin da take jiran Manchester City da Bayern Munich da za su kara.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG