Ra'ayoyin Matasan Nijar Akan Shugaban Kasarsu da Nada Dansa

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

Matasan kasar Nijar sun bayyana ra'ayoyinsu dangane da nadin da shugaban kasarsa Muhammad Issoufou ya yiwa dansa da ya bashi wani mukamin siyasa

Mutumin farko yace idan shugaban kasa ya ga dansa zai yi abubuwan da zasu gyara masa mulki yana iya nadashi kan mukami musamman mukami dake kusa dashi ko cikin fadarsa.

Wani yace nada danshi a aofishin sadarwa abu ne mai jiwuwa saboda manyan mutane suna da 'yancin su zabi wanda suka fi yadda dashi. Ftansa shi ne Allah ya sa dan shugaban kasar ya yi rike mukamin yadda ya kamata.

Wani ya ce kodayake doka bata hana ya nada dansa ba kuma mukamin na bukatar wanda shugaba ya fi yadda dashi, amma duk da haka nadin tamkar akwai lauje cikin nadi ne. Da ya samu wani wanda ba dansa ba ne.

Wani yace yakamat shugaban kasa ya dinga neman shawara kan duk abun da zai yi. Idan yaron ya mallaki hankalinsa yana iya aikin idan kuma bai mallaki hankalinsa ba to bai dace ba a nadashi mashawarcin shugaban kasa. Yace tuwona maina bai yi ba.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ra'ayoyin Mtasan Nijar Akan Shugaban Kasarsu - 2' 04"