Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron tsaro a Nijar ya ce samarwa matasa aiki shi ne mafita rikicin Boko Haram


Kungiyoyi daga kasashen dake yankin tafkin Chadi ne suka yi taron neman zaman lafiya a kasashensu dake fama da rikicin 'yan ta'adan Boko Haram

Samawa matasa aikin yi na cikin matakan da mahalarta taron da wasu kungiyoyi daga kasashen yankin tafkin Chadi suka yi akan rikicin Boko Haram da ya addabi yankinsu.

Malam Musa Cangari na wata kungiya da ta halarci taron yace kowa ya amince cewa idan har ana son a fita daga fitinar da Boko Haram ta haddasa dole ne a yi nazarin yadda za'a samarma matasa aikin yi saboda idan matasa basu da aikin yi suna iya shiga rikici.

An kuma amince a taron cewa duk abubuwan da ake yi yakamata a yi tare da shawara da jama'a da wakilansu ko sarakunan gargajiya ko wadanda suka zaba ya zamanto ana shawara ana jin maganar da mutane suke yi. Idan aka kiyaye da wadannan mataki zasu taimaka wajen shawo kan fitinar Boko Haram.

Muhammad Shuwa magatakardan kungiyar sarakunan gargajiya daga Najeriya cewa ya yi sun gamsu da shawarwarin da aka tsaya a taron kuma zasu kaiwa na gabansu labari tare da tattara jama'arsu idan sun koma gida domin su fadakar dasu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG