Rasha Ta Yi Bikin Tunawa Da Karshen Yakin Duniya Na Biyu

Firai Ministan Rasha Vladimir Putin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar

Kasar Rasha ta baje kolin faretin rundunonin sojojinta a jiya a birnin Mascow don bikin cika shekaru 70 na nasarar da suka samu a ranar kasashen Turai da aka fi sani da VE Day.

A rana irin ta jiyan ne ‘yan mayakan Nazi suka ajiye makamansu a shekarar 1945 tare da mika wuya wanda kuma ya kawo karshen yakin duniya na biyu.

Shugaban kasar Vladimir Putin ya godewa manyan kasashen da suka mara wa kasar Rasha baya kamar su Amurka, Birtaniya da Faransa don murkushe ‘yan Nazi.

Bikin dai ya gudana ne a kasar Rashan duk da la’akari da goyon bayan kasashen yammaci ga kasar Ukreine game da kwace yankin Kirimiya da Mascow tayi tare da zargin shugaban kasar da marawa ‘yan aware masu kisa.