Rawar Da Sojoji Suka Taka A Zabe Itace Inganta Tsaro

Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai.

Da yake magana yayin wani taron manema labaru a Abuja, kakakin kungiyoyin fararen hulan kasar, Clement Nwankwo ya ce ba suji dadin yadda ake amfani da sojoji ba, wurin hada hadar samar da tsaro a harkokin zabe a kasar, al'amarin da ya ce ya sabawa shika-shikan tsarin demokradiyya.

kungiyoyin fararen hular suka ce dole ne a duba a ga menene akeyi ba dai-dai ba domin gano yadda za a gudanar da sahihin zabe marasa rikici a cikinsa ba tare da sa hanun sojoji wurin samar da tsaro ba.

Da yake mayar da martani yayin da tawagar jami'an tarayyar turai suka ziyarce shi a ofishinsa, babban hafsan hafsoshin rundunar sojojin Najeriya, Laftanar Janaral Tukur Buratai ya ce sojoji na aiki ne bisa kwarewa tare da bin ka'idoji kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar masu.

Janaral Tukur Buratai ya kara da cewa mutanen da ba sa wa Najeriya fatan alheri ne kadai kuma suke amfana da duk wani yamutsin zabe, ke korafin yadda sojoji ke marawa hukumomin fararen hula musamman ma 'yan san baya, wajen gudanar da aikin tsaro, yana mai cewa ba wani rawa na musamman da sojojin ke takawa yayin zaben, amma suna dai zaman jiran ko takwana ne don marawa kokarin 'yan sanda.

Yanzu haka dai ana ci gaba da tafka muhawara dangane da rawar da sojoji ke takawa wajen samar da tsaro, yayin zabubbuka a Najeriya na ci gaba da janhankalin masana, kwararru da ma kungiyoyin fararen hula.

Your browser doesn’t support HTML5

Rawar Da Sojoji Suka Taka A Zabe Itace Inganta Tsaro 2'20"