Real Madrid Da Man City Sun Tashi 1-1

Haaland, hagu da Vinicius, dama (Hoto: AP)

A mako mai zuwa za a buga zagaye na biyu a Manchester inda kowace kungiya za ta san matsayinta.

Real Madrid ta yi kunnen doki da abokiyar hamayyarta Manchester City inda aka tashi da ci 1-1 a gasar Zakarun Nahiyar Turai.

Vinicius Junior ne ya fara zura kwallo a minti na 36 kafin a tafi hutun rabin lokaci a wasan wanda aka a matakin semi-final.

Kevin de Bruyne ne ya farke wa City kwallon a minti na 67.

Vinicius ya zura kwallonsa ne a saman gefen ragar City da ta ziyarci Madrid a zagayen farko na wannan wasan.

Shi kuwa De Bruyne doka kwallon ya yi da karfin tuwo ya farke kwallon bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

A mako mai zuwa za a buga zagaye na biyu a Manchester yayin da za kuma a buga daya wasan semi-final tsakanin Inter Milan da AC Milan a ranar Larabar wannan mako.