Rigakafin Cutar COVID-19 Ba Zai Kawo Karshen Cutar Ba - Hans Kluge

Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya reshen Turai ya ce hukumarsa ta yi hasashen za a samu karuwar mace-mace sanidiyyar cutar COVID-19 a watannin Oktoba da Nuwamba. 

A wata hira da kamfanin dillacin labarai na AFP a ranar Litinin 14 ga watan Satumba, Hans Kluge ya ce, "lamarin zai yi muni, a watan Oktoba da Nuwamba za a ga karin mace-mace. ”

Kluge ya kuma yi gargadin cewa rigakafin cutar ba zai kawo ƙarshen cutar ba. Ya ce "a ko da yaushe ina jin cewa: 'rigakafin zai kawo ƙarshen cutar, “ba haka ba ne!" a cewarsa.

"Ba mu ma sani ba ko rigakafin zai yi aiki kan kowa. Muna samun wasu alamu a yanzu da ke nuna cewa rigakafin zai taimaka wa wasu mutane amma banda wasu,” in ji shi.

Ya kara da cewa kuma idan za mu samar da riga kafin dabam-daban, aikin da wahala.

Kluge ya ce abinda zai kawo karshen annobar shine lokacin da mu a matsayin mu na al'ummomi za mu koyi yadda zamu ci gaba da rayuwa da annobar.