Rikicin Burundi ya kusa kaiga tabarbarewar doka da oda kwatakwata

'Yansandan kasar na cigaba da harbe mutane

Shugaban hukumar kare hakkin dan dama a Majalisar Dinkin Duniya, ya yi gargadi game da karin tashe-tashen hankula da ake ci gaba da samu a Burundi, lamarin da ya ce na gab da haifar da rashin doka da oda a kasar.

Shugaban hukumar, Zeid Ra’ad Al Hussein, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, yana mai cewa wasu samame da jami’an tsaron kasar suka kai a ranar 11 ga watan Disamba akan ‘yan adawa, sun keta hakkin bil adama.

Ya kara da cewa rahotanni sun nuna cewa a lokacin samamen an yiwa mata fyade kana akwai bayanai da ke cewa an ga wasu manyan kaburbura da aka binne mutane a yankin.

Al Hussein ya kuma ce wannan rahoto ne da ke nuna alamun cewa an dauki hanyar fadawa rikicin kabilanci.

A ranar 12 ga watan Disamba, dakarun kasar ta Burundi suka bayyana cewa an kashe mutane 87 a Bujumbura, babban birnin kasar, bayan wani hari da su ka yi ikrarin an kai akan a wasu sansanoninsu.

Sai dai wadanda suka shaida lamarin a yankin, sun yi zargin cewa har gida jami’an tsaron suka bi mutanen suka kashe su.