Rikicin Siyasa ya Barke a Jihar Ekiti

An kafa dokar hana fita a Ado Ekiti, babban birni jihar,

An kafa dokar hana fita a Ado Ekiti, babban birni jihar, Gwamnar jihar Dr, Kayode Fayemi, ne ya bada ummarni haka sanadiyar wani rikicin siyasa da ya barke tsakanin magoya bayan jamiyar PDP da na APC.

Rikicin dai yakara kamari ne bayan da aka kashe shuigaban kungiyar direbobi ta kasa reshen jihar ta Ekiti Chief Omolafe Adereye.

Gwamna Fayemi ya ci gaba da cewa tunda jami’an tsaro na kan lamarin ya bukaci da sun iya yinsu wajen kare dukiyoyi da rawukan alumar kasar.

Shi kuwa gwamna mai jiran gado Mr. Ayo Fayose, cewa yayi abun ya kasance abun takaice, ya kuma ummarci jama’a da kada sun dauki doka a hannun su.

Your browser doesn’t support HTML5

Rikicin Ado Ekiti - 1'27"