Rundunar Sojin Najeriya Ta Kai Tallafin Kayan Karatu Wasu Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira

Rundunar Sojan Najeriya Ta Kai Tallafin Kayan Karatu Sansanonin 'Yan Gudun Hijira

A wani yunkuri na tallafawa yara yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya shafa, rundunar sojin Najeriya ta kai tallafin kayayyakin karatu da na rubutu ga dubban yara dake sansanonin yan gudun hijira dake jihohin Adamawa da Taraba.

Alkalumman hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, sun nuna cewa Boko Haram ta raba fiye da yara miliyan daya da digo hudu daga gidajensu a Najeriya da makwabtanta.

Baya dai ga asarar rayuka da dukiya da rikicin Boko Haram ya janwo a jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya, yanzu haka wata matsalar itace ta harkar ilimi, inda kawo yanzu akwai dubban yara yan makaranta dake gudun hijira a sansanonin da aka tanadar.

To sai dai kuma a wani yunkuri na tada komadar ilimin kananan yaran da tashin hankalin Boko Haram ya raba da gidajensu, yanzu haka rundunar sojin Najeriya ta horar da malaman dake karantarwa a makarantun wucin gadi tare da bada tallafin karatu na dubban Nairori.

Rundunar Sojan Najeriya Ta Kai Tallafin Kayan Karatu Sansanonin 'Yan Gudun Hijira

A wajen bikin bada kayayyakin karatu biyo bayan kamala horon kwanaki uku da aka shiryawa malaman, mukaddashin kwamandan rundunar soji na 23 dake Yola, Brig. Gen. Benson Akinroluyo, yace an dauki wannan mataki ne don zaburar da malaman dake tallafawar da suma kansu daliban wanda ciki har da manya dake karatun yaki da jahilici.

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, itace ke kula da sansanonin yan gudun hijiran kuma ta bayyana farin cikin ta da tallafin da rundunar sojin ke badawa.

Sa’ad Bello shine jami’in hukumar NEMA mai kula da jihohin Adamawa da Taraba, ya bayyana farin ciki game da wannan yunkuri na ganin an taimaka wajen ganin an bunkasa ilimi a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Malama Fatima Hassan na cikin iyaye yan gudun hijira a sansanin Malkohi, tace yanzu haka sun fara cin gajiyar shirin karatun ganin cewa yayansu sun fara iya karatu da rubutu.

Masana hallayar dan Adam na kira ne da a hada hannu domin suma wadannan yara kada a barsu a baya, batun da gwamnatin jihar Adamawa ta bakin babban sakataren ma’aikatar ilimi Mahmud Abubakar ke cewa zasu tallafa.

Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kai Tallafin Kayan Karatu Wasu Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira - 3'24"