Rundunar Sojojin Najeriya Ta Kori Wasu Sojoji

Manjo-janar Chris Olukolade kakakinrundunar sojojin Najeriya

Rundunar Sojojin Najeriya ta kori wasu sojoji guda tasa'in daga bakin aiki

Rundunar ta ce ta samesu da laifin rashin da'a yayin da suke bakin aiki wurin fafatawa da 'yan kungiyar Boko Haram.

To saidai sojojin da aka kora wadanda suke zaune a barikinsu dake Ilorin cikin jihar Kwara sun nuna damuwa da matakin da rundunar ta dauka akansu. Sun bayyana matakin a matsayin yi masu danniya.

Saidai rundunar ta hikance an koresu ne saboda samunsu da laifin yin rashin da'a, da rashin bin umurni irin na soji. Rundunar ta ce a dokar aikin soja lamarin haka yake.

To amma da suka kira wakilin Muryar Amurka sojojin da aka kora sun ce an turasu dajin Sambisa domin yakar Boko Haram amma ba'a basu makamai ba. Sun yi fada da Boko Haram har kayan aikinsu suka kare amma ba'a basu kari ba. Jirgin saman yaki dake rufa masu baya ta sama sun kira ya ki zuwa.

Amma mai magana da yawun rundunar Kanal Timothy Antuga ya bayyana dalilan korar sojojin. Yace an kori wasu sojoji daga bakin aiki saboda rashin biyayya da wasu halaye marasa kyau a yakin da ake yi da 'yan ta'adan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Kori Wasu Sojojinta - 2' 55"