Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Sake Karbe Garin Marte


Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.

Al'umar birnin Maiduguri na ci gaba da korafi kan irin mawuyacin halin da suka shiga tun bayan da aka saka dokar hana fita. Hakan kuma na faruwa ne bayan da rahotanni ke nuna cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun sake kwace garin Marte.

Rahotanni daga Najeriya na cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun sake karbe ikon garin marte da ke jahar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Mataimakin gwamnan jahar Alhaji Zanna Umar Mustapha ne ya tabbatarwa da manema labarai hakan ne a lokacin da ya ke baiwa al’umar jahar hakuri kan dokar hana fita da aka kafa a garin.

A cewars an saka dokar ne da izninsu bayan da dakarun Najeriyar suka ce akwai wasu mutane kimanin 60 da ke shirin kai hari a garin na Maiduguri.

“Mu dai abin da za mu cewa jami’an tsaro shi ne su san inda za su shiga domin yanzu yaran nan sun san cewa ana biye da su, za kuma su iya yiwa mutane komai, tunda sun san cewa mutuwa ta zo kuma karshen yakin ya zo.” In ji mataimakin gwamnan.

Ya kuma kara da cewa an sake karbe garin na Marte ne saboda a lokacin da dakarun Najeriya suka kwato garin mutane kadan ne suka koma, hakan kuma ya ba mayakan karfin sake komawa garin.

A yau Asabar rundunar tsaron Najeriyar ta ce ta sassauta dokar wacce za ta fara aiki daga karfe biyar na maraica zuwa karfe takwas na safe.

Yanzu haka mutanen garin na Maiduguri suna ta nuna korafinsu kan wannan dokar hana fita domin a cewarsu wasu su ba su ma san halin da suke ciki ba.

“Abinda ya faru a Borno mu ba mu ma san abin da muke ciki ba, muna cikin dokar ta baci ne ko kuwa ba haka ba, mu bamu ma sani ba, yanzu an je wani kauye dake da tazarar kilomita hudu daga Maiduguri an kashe mutane sama da 20 an kwashe musu shanu amma a ce babu wanda ya gansu.” In ji wani mazaunin garin da ya zanta da wakilin Muryar Amurka.

Ga karin bayani a rahoton Haruna Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG