Sabuwar Jam'iyyar Jubilee Party Ta Hadiye Jamiyyu 11 A Kenya

Uhuru Kenyatta, shugaban Kenya

Dubun dubatar magoya bayan shugaba Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William ruto ne, suka taru a babban filin wasa na birnin Nairobi, yayin da aka kaddamar da sabuwar jam’iyar Jubilee Party, wacce aka dunkule ta da wasu jam’iyyu 11.

Wannan matakin hadewar jam’iyyun a karkashin lema guda, na zuwa ne shekara guda kafin zaben shugaban kasar da za a yi.

Shugaba Kenyatta ya bayyana cewa hadin kai shi ne maksudin hadewar jam’iyyu wuri guda, inda ya ce “wannan jam’iyya da muka kaddamar, wata alama ce ta hadin kai, wadda ta nuna hadin kan ‘yan kasar Kenya.”

Sai dai masu lura da siyasar kasar sun ce kaddamar da sabuwar jam’iyyar, batu ne kawai da ke bayyana a fatar baka.

Domin a cewar shugaban sashen nazarin kimiyyar siyasa a jami’ar Nairobi, Adams Oloo, wannan gangami, wata kafa ce kawai da shugaba Kenyatta da mataimakinsa Ruto, su ka yi amfani da ita domin kaddamar da yakin neman a sake zabensu, da kuma nufin dinke barakar da ka iya faruwa a shekara mai zuwa.