Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar zaben Kenya zata gyara kurakuran zaben shekarar 2013 kafin zaben badi


Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta

Wani kusa daga Hukumar Zaben Kasar Kenya mai zaman kanta da kuma Hukumar Kula da kan iyakoki yace, hukumar zaben tana son inganta ayyukanta ta hanyar la’akari da zaben shekarar 2013, saboda shirye-shiryen zaben kasar da za a yi a badi.

Kundin tsarin mulkin kasar dai ya bukaci za’a yi zaben kasar ta Gabashin Afirka ne a ranar 18 ga watan Agustan shekarar 2017 in Allah ya kaimu. Jami’an hukumar zaben sun ce suna aiki da masu ruwa da tsaki don nuna damuwarsu da zaben zagaye na biyu a zabuka.

Yusuf Nzibo na cikin manyan hukumar zaben, ya kuma ce, suna nan suna aiki da‘yan kasashen waje don gyara kurakuran da aka yi a baya lokacin zaben na shekarar 2013 na kasar.

Wannan jawabi na Nzibo ya fito ne daga bakinsa lokacin da wasu kungiyoyin fararen hula suka yi zanga-zanga a gaban ofisoshin zaben kasar, bisa zargin hukumar da cewa ta gaza aiwatar da sahihin zabe a shekarar ta 2013 da ta shude.

Masu zanga zangar sun bukaci a rushe hukumar zaben domin a nada wata sababbin da zata yi aikin da gaskiya. Ya kara da cewa ‘yan adawa ma sun yarda da matakin kotun koli bayan kungiyoyin sun kalubalanci zaben a hukumance.

XS
SM
MD
LG