Sai Inda Karfinmu Ya Kare Wajen Taimakawa Al'umar Texas - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump

Al'umar jihar Texas da bala'in ambaliyar ruwa ya afkawa, na ci gaba da samun tabbaci daga hukumomin kasar kan tallafa masu da za a yi domin su koma rayuwarsu ta da yayin da shugaba Donald Trump ya ce har ya fara magana da wasu 'yan majalisar dokokin kasar.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi alkawarin agaza wa mutanen Texas da Louisiana domin ganin sun samu saukin bala’in da ya auka musu na ambaliyar ruwa.

Shugaba Trump ya shaidawa taron ‘yan jarida a Fadar White House jiya Litinin cewa wadanda wannan lamari ya rutsa da su, su kwana da sanin cewa za su samu taimakon gaggawa nan ba da jimawa daga majilisar dokokin kasa domin samun kudin da suke bukata don kimtsa gidajen su da ruwa ya mamaye.

“Za ku samu duk abinda kuke bukata, kuma cikin gaggawa, na riga har na fara tattaunawa da wasu ‘yan majalisar dokoki, sun kadu da irin halin da 'yan jihar Texas kuke ciki.” In ji shugaba Trump.

Shi ma shugaban hukumar ba da agajin gaggawa Chief Brock Long ya shaidawa manema labarai a jiya cewa hukumar za ta dauki shekaru tana aiki a Texas.

Long ya ce yanzu haka hukumar ta fara shirin aiki na tsawon lokaci, irin wanda ta jima ba ta yi irinsa ba.