Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kori Admiral Joseph Aucoin Daga Bakin Aiki Saboda Rashin Ingancin Shugabancinsa


A jiya Talata ne ofishin yada labaran fadar shugaban Amurka ta sanar da mutuwar matukan jirgin ruwan yakin Amurka guda 10 a wani hadari da ya faru.

Rundunar sojan ruwan Amurka ta kori kwamandan tawagar jiragen ruwanta ta 7 bayan wasu hadurra da dama na cin karo da wasu jirage a teku da suka faru, ciki harda hadarin da ya faru shekaranjiya litinin wanda a cikinsa sojojin jirgin ruwan Amurka guda 10 suka rasa rayukkansu.

Kwamandan sojan ruwa Admiral Scott Swift shine yanzu aka nada don ya maye gurbin Admiral Joseph Aucoin yau Laraba, bayanda hukumomin sojan kasar suka bayyana abinda suka kira “rashin amincewa da ingancin shugabancin sa na jagorancin irin wannan rukunin na sojan ruwan.

Dama a watan Janairun da ya gabata ya kamata Aucoin yayi ritaya, amma aka dage bayan da jirgin ruwan USS John S McCain ya zamo jirgin ruwan yaki na sojan Amurka na biyu da ya kara da wani jirgin dakon kaya a watannin baya.

Facebook Forum

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG