Sakataren Gwamnantin Tarayyar Najeriya Ya Musanta Zargin Kakakin Majalisar Dattawa

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki

Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Injiniya David Babachir Lawal ya musanta zargin da Kakakin Majalisar Dattawan Najeriya ya yi cewa da hannun gwamnati wajen gurfanar dashi da mataimakinsa gaban kotu akan wai, sun canza dokokin majalisar lokacin da aka zabesu.

Bisa ga alamu za'a dade ana kai ruwa rana game da dambarwar majalisar dattawan Najeriya akan batun shari'ar da ake yiwa Dr Bukola Saraki kakakin majalisar dattawa da mataimakinsa, Ike Ekweremadu.

An zargi shugabannin majalisar ne da sauya dokokin majalisar kafin a zabesu a shekarar da ta gabata.

Batun gurfanar dasu gaban kotu ya jawo cecekuce a ciki da wajen Najeriya inda wasu suna ganin abun da ita APC ta yiwa PDP aka mayar mata a zaben shugabannin majalisun yanzu.

Tun farko Sanata Bukola Saraki, kakakin majalisar ya ce akwai hannun gwamnatin tarayya akan lamarin da suke fuskanta.

Amma yayinda yake yiwa manema labarai jawabi a Yola babban birnin Adamawa, sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Injiniya Bababchir David Lawa yace babu hannun gwamnatin Buhari a cikin lamarin. Yace abun mamaki ne a ce akwai bita da kulli a sharia'r da kakakin da mataimakinsa ke fuskanta a kotu. Yace sanatoci su ne suka yi zargi. Su suka rubutawa 'yansanda su binciki lamarin. Sun ce dokar da aka yi anfani da ita wajen zaben shugabannin ba dokar ainihi ba ce, an canzata.

Bayan da 'yansanda suka gama bincikensu sun mika wa atoni janar na kasar rahotonsu inda suka tabbatar an canza dokokin da aka yi anfani dasu wurin zaben. Yace abun dake faruwa yana tsakanin shugabannin majalisar da sanatocin majalisar ne.

Alhaji Idris Ardo tsohon dan jarida yana ganin akwai abun dubawa a lamarin.Yace lokacin da aka zabi Waziri Tambuwal a matsayin kakakin majalisar wakilai 'yan adawa da wasu 'yan PDP, jam'iyyar dake mulki, suka hada kai suka zabeshi. Suna ganin bai kamata jam'iyyar dake mulki ta ce ga wanda za'a zaba kakakin majalisar ba. Yace wannan tsarin ne ya cigaba inda majalisa tana neman tabbatar da 'yancinta. Yace abun da jam'iyyar APC ke so daban abun da 'yan majalisa kuma suke so daban shi ya kawo takaddamar.

Wani mai fashin baki akan harkokin majalisa Dr. Ahmed Bawa Bello na ganin ko ba komi wannan cigaba ne a fagen dimokradiyar Najeriya. A dimokradiya ba dole ba ne shugaban kasa ya samu abun da yake so koyaushe ba. Haka ma ita majalisa ba dole ne ta samu abun da take so koyaushe ba. Yace kundun tsarin mulki ya ba kowa cin gashin kansa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Sakataren Gwamnantin Tarayyar Najeriya Ya Musanta Zargin Kakakin Majalisar Dattawa - 4' 28"