Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya Ya Fatattaki Wakilin Ministan Shari’ar


Sanata Bukola Saraki, Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

Har yanzu tsuguno bata kare ba, domin kuwa ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin Ministan Shari’a na Najeria da Majalisar Dattawan kasar game da shari’ar shugaban Majalisar.

A karo na biyu Ministan Shari’ar kasar, Abubakar Malami ya ki bayyana a gaban kwamitin kula da harkar shari’a na majalisar dattawa domin su binciki gurfanar da shugabannin majalisar da aka yi a farkon makon nan.

Koda ya ke Fadar shugaban kasar ta tura wani wakili a madadin ministan, to amma kuma sai aka fatattakeshi daga Majalisar da cewa, su Mai Shari’a Abubakar Malami suke bukata ba Mashawarcin Shugaban kasa a game da harkar shari’a ba.

Mista Obula ya fusata kwarai bayan fatattakar da aka yi masa, inda ya cewa wakiliyarmu ta Muryar Amurka a Majalisa Madina Dauda jawabi cikin fushi da cewa kawai sun so yankwana su ne bisa takama da majalisa.

Shima daya daga cikin ‘yan Majalisa Joshua Ludani ya bayyana matsayar da kwamitinsa ke ciki da kuma dalilin da yasa aka bukaci Ministan Shari’ar ya hallara a gabansu game da shari’ar shugaban Majalisar Abubakar Bukola Saraki.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:48 0:00

Bidiyo

Mijin Aljana A Kano: Shin Dama Aljanu Na Da ATM’ Na Kudi?
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG