Sashin Majalisar Dinkin Duniya Yayi Ikirarin Cewa Kazantarciyar Iska Na Kawo Cutar Kansa

Iskar kamfanoni da sauransu na iya kawo cutar kansa

Iskar da muke shaka tana hade da abubuwan dake kawo cutar kansa, kuma ya kamata a bayyana su a matsayin masu hadari ga mutane, hukumar lafiya ta duniya ta sashin kansa ce ta bayyana haka.
Iskar da muke shaka tana hade da abubuwan dake kawo cutar kansa, kuma ya kamata a bayyana su a matsayin masu hadari ga mutane, hukumar lafiya ta duniya ta sashin kansa ce ta bayyana haka.

Kungiyar bincike kan cutar kansa ta duniya ta nuna bayanai akan cewa a 2010, a dukan duniya baki daya, an sami mutuwar mutane 223,000 sakamakon cutar kansar huhu wanda ya zama sakamakon kazantarciyar iska, kuma suka ce akwai karuwar alamu na hadarin cutar kansar mafitsara.

Hukumar lafiya ta duniya wadda take a Geneva – wanda aikinta ya kunshi bukatun lafiya na jama’ar duniya.

Kazantarciyar iska, wadda yawanci lokaci take samuwa ta dalilin tafiye tafiye, harkokin samar da wutar lantarki, iskar kamfanoni ko aikin gona da girke-girke na gidaje, suna taimakawa wajen kawo yawan cututtuka dake da dangantaka da shakar iska da cututtukan zuciya.

Bincike ya nuna a wadannan shekarun, fuskantar irin wannan ya karu sosai a sassan duniya da yawa, musamman kasashe masu al’umma da yawa tawurin karuwar kamfanoni kamar a China.

Kungiyar kimiyya ta baiyyana yawancin magungunan kimiyya na hade da abubuwan kazantar iska, hadi da iskar injina, kura da sauransu. Amma wannan ne lokaci na farko da masana suka baiyyana kazantacciyar iska cewa tana kawo cutar kansa.