Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Allurar Rigakafin HIV Yana Kara Hadarin Cutar


Dakin binciken cutar HIV
Dakin binciken cutar HIV

A fadar masanan kimiya, bayani na karuwa cewa maganin da ake gwaji domin kiyaye mutane daga kwayar cutar virus yana kara hadarin kamuwa da cutar.

A fadar masanan kimiya, bayani na karuwa cewa maganin da ake gwaji domin kiyaye mutane daga kwayar cutar virus yana kara hadarin kamuwa da cutar. An baiyyana sakamakon wannan bincike a fili lokacin taron maganin cutar kanjamau na 2013 a birnin Barcelona na kasar Spain.

Haka kuma, masana a kasar Rusha sun shaida cewa sun gano wani sabon jinsi a cutar ta kanjamau mai karfi sosai. Irin wannan jinsin, da aka lakamawa suna 02_AG/A, yana yaduwa da sauri kuma yanzu an ce ita ce ta kai ga kashi 50 bisa dari na sababbin cutar kanjamau a kasar Siberia.

Wannan kwayar cutar an fara ganinta a birnin Novosibirsk cikin 2006, kuma an yi tunanin cewa ita ce kwayar cuta da tafi yawa a kasar Rusha. Bisaga labarai daga Moscow, masanain cutar dake dangin Virus da kuma binciken yadda cutututtun ke kama mutum dake na yankin Saberiya sune suka gano wannan kwayar cutar mai karfin gaske. Natalya Gashnikova, shugaban wannan sashi na binciken yace, 02_AG/A zai iya yaduwa cikin jama’a da sauri sosai fiye da sauran jinsin kwayar cutar HIV wadanda ake dasu a kasar Rusha.

Yawan mutanen dake dauke da cutar HIV a Novosibirsk ya tashi daga 2,000 a 2007 zuwa 15,000 a 2012, bisa ga wurin bincike na cutar kanjamau na kasar Rusha kuma ya nuna cewa kashi 50 daga cikin dari na sababbin yaduwar ya samu ne tawurin jinsin kwayar cutar mai suna 02_AG/A.

Ba a Sibriya kadai ake samun irin wannan sabon jinsin na kwayar cutar ba, ana samun sa a Chechnya, a kudancin Rusha, da Kyrgyzstan da Kazakhstan.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG