Guguwa tayi munmunar barna a wasu jihohin Amurka.

Wata motar 'yan kwana-kwana na shawagi a kusa da wata unguwar Rowlett, a jihar Texas, bayan wata Guguwa da tayi barna, har mutane 11 suka rasa rayukan su, da dama kuma suka jikkata. A ranar 27 ga watan Disamba 2015.

Wata mota  kusa da gidana Antonio Yzaguirre, mai shekaru 70,
da matar shi Ann Yzaguirre, mai shekaru 69, a ranar Alhamis 24, ga watan Disamba, an samesu a cikin gidan su, sun mutu, bayan wata guguwa da tayi barna a daren Laraba, haka kuma mutane 7 sun mutu a jihar  Mississippi.

Mutane ke gugun tsira da rai a dai-dai lokacin da aka daka wata tsawa, a tsakiyar babban birnin Dallas. Hukumomin kula da yanayi sun bayyanar da cewar garin Dallas na cikin wani mumunan yanayi, a ranar 26, ga watan Disamba.

Walkiya kenan a lokacin da guguwa ta taso a karamar hukumar Jefferson, wanda tayi barna a wasu gidaje, ranar Juma 25 ga watan Disamba.

Barnar da guguwa tayi kenan a unguwar Bermingham, a jihar Alabama, a ranar 26 ga watan Disamba 2015. Guguwar dai ta rusa gidaje kuma ta tunbuke bishiyoyi. Haka kuma mutane 3 sun samu rauni a garin da yafi yawan mutane a jihar, a cewar jami'an 'yan sanda da masu aikin agaji.

Wata mata Tanager Tyler da danta Mitchell suna kallon wata mota a ranar Asabar 26, ga watan Disamba, wadda ta birkice a dai-dai hanyar shiga gidan su.