Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Ruwanda Paul Kagame Zai Tsaya Takara Karo Na Uku


Paul Kagame
Paul Kagame

Sabon sauyin da aka yi a kasar Ruwanda zai ba shugaban kasar mai mulki yanzu Paul Kagame damar sake tsayawa takarar shugabancin kasar karo na uku.

Shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame, ya ayyana shirinsa na tsayawa takara a wa’adi na uku a shekarar 2017, mako guda bayan da kasar ta gudanar da zaben raba gardama kan yin sauyi ga kudnin tsarin mulkin kasar.

Shugaba Kagame ya bayyana hakan ne a wani jawabinsa na sabuwar shekara da ya yiwa ‘yan kasar ta kafar Talbijin, yana mai cewa ganin irin muhimmanci da ‘yan kasar suka nuna kan wannan batu, babu abinda zai iya yi, illa ya amince da bukatunsu.

Sai dai shugaban na Ruwanda ya ce, ba shi da burin ya ga kasar ta dauki hanyar samun shugaban kasa da zai zauna a kan karagar mulki har iya rayuwarsa.

A ranar litinin din da ta gabata, Kagame ya mika godiyarsa ga al’umar kasar, bayan da suka amince da sauyin kundin tsarin mulkin da zai kawo canji kan yawan wa’adin da kowane shugaba zai yi.

Wa’adin Kagame mai shekaru 58, zai kare ne a karshen shekarar 2017, sai dai sabon sauyin da aka yi, zai bashi damar yin wani wa’adin shekaru bakwai da kuma wani wa’adin shekaru biyar da zai biyo baya, wanda hakan zai bashi damar zama kan karagar mulki har nan da zuwa shekarar 2034

XS
SM
MD
LG