Shin Shiga Yajin Aikin da Kungiyar Kwadago Tayi Ba Rena Kotu Ba Ne

Masu zanga zanga

Shiga yajin aiki da kungiyar kwadago tayi bayan da kotu ta gaya mata kada tayi wato ta rena kotu ke nan?

Shiga yajin aikin da kungiyar ta yi ya hadu da fushin bangaren zartaswa wadda ta nemi dakatar da ita soboda ta ruga kotu inda ta shigar da kara.

Kwana daya kafin ta shiga yajin aikin gwamnatin tarayya ta ruga je ta nemi hana yajin aikin. Kotun ma'aikata dake Abuja ta amince da bukatun gwamnatin tarayya ta kuma bada umurnin kada kungiyar kwadagon ta shiga yajin aiki. Gwamnati zata babbatar doka tayi aikinta.

Saidai kungiyar tace ita bata ga takardar sammaci ba kafin ta fantsama yajin aiki. Wai sai mutum ya ga takarda ne zai bi umurnin kotu.

Lauya Hassan Liman ya bada bahasi akan hukuncin kin bin umurnin kotu. Duk inda kotu ta bada umurni wajibi ne a bi umurnin domin idan ba'a bi ba laifi ne a karkashin doka. Kotu kuma na iya hukumta wanda ya kaucewa umurninta.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shin Shiga Yajin Aikin da Kungiyar Kwadago Tayi Ba Rena Kotu Ba Ne - 10' 06"

Kafin ta janye yajin aikin gwamnati ta bakin antini janar nata Abubakar Malami yace gwamnati ba zata lamunta da irin hakan ba. Yace lamura ne da suka jibanci da'a da doka da oda kuma a akasarin gaskiya duk abun da mutum zai yi a matsayinsa na dan kasa doka tayi tanadi.Idan kuma ya kaucewa da'a kan tsari to yana iya ganin abun da baya so.