Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Najeriya Kungiyar Kwadago Ta Lashi Takobin Fantsama Yajin Aiki Yau Laraba


Kungiyar Kwadago ta Najeriya tana ci gaba da bayyana rashin amincewarta da janye tallafin mai da gwamnati ta yi a kasafin kudin bana
Kungiyar Kwadago ta Najeriya tana ci gaba da bayyana rashin amincewarta da janye tallafin mai da gwamnati ta yi a kasafin kudin bana

Duk da umurnin da kotun dake kula da dokokin ma'aikata a Najeriya ta bayar cewa kada kungiyar kwadago ta shiga yajin aiki yau, kungiyar ta fito karara cewa zata fara yajin aikin har sai gwamnati ta janye karin da ta yiwa farashen man fetur

A Najeriya, kungiyoyin kwadago da na fararen hula har yanzu suna shirin ci gaba da shiga yajin aiki yau Laraba, saboda kara farashin mai, duk da umarnin da kotu ta bayar na hana su yin haka.

Babbar kungiyar kwadago, da kuma kungiyar ma'aikata masu sana'o'in hanu da ake kira TUC, wadanda suka ce suna wakiltan ma’aikata miliyan shida da rabi, da wasu kungiyoyin farar hula sun nemi ma'aikata su shirya yajin aikin ne saboda karin farashin mai dalilin janye tallafi, da kuma karancin kudaden kasashen waje.

Ana ci gaba da shawarwari tsakanin gwamnati da kungiyoyin da nufin dakile yajin aikin, amma babu rahoton an sami ci gaba.

Abiodun Aremu,babban sakataren hadakar kungiyoyin kwadago dana farar hula, yace tilas gwamnati ta janye karin farashin man, kamin a cimma wata matsaya da 'yan kwadagon.

XS
SM
MD
LG