Shirin Samar Da Guraren Kiwo Ga Fulani Makiyaya A Najeriya

Shanun Fulani.

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin samar da guraren kiwo ga Makiyayan kasar, domin shawo kan matsalar tashin hankali a tsakanin Manoma da Makiyaya a kasar

A yanzu dai gwamnatin ta kafa wata tawaga ta musamman da ke ran gadin jihohin Najeriya, domin fadakarwa akan muhimmancin samar da guraren kiwo ga Makiyayan. ‘daya daga cikin tawagar kuma darakta na ma’aikatar gona ta Najeriya, Alhaji Mohammadu Dan Lami Salihu, yace gwamnatin Najeriya na kokarin taimakwa gwamnatocin jihohi domin ganin an baiwa masu gonaki shawara da cewa su dai na yin shuka har zuwa gabar kwalta, domin samar da hanya ga dabbobi. Haka kuma suma Makiyaya su daina yawo da daddare da dabbobi.

Baya ga batun samar da makiyayar dabbobin dai akwai batun matsalar shawo kan satar Shanu, da ta addabi Fulani. Hardon Zuru Alhaji Mohammadu Kirwa, shugaban kungiyar makiyaya ta Myetti Allah, yace sun fito da wani sabon shirin bayar da takarda ga duk wanda ya sayi Saniya a Kasuwa, don kawo karshen wannan matsala.

Shugaban hada kan matasan Fulanin Najeriya, Alhaji Bello Mohammad Garatu, yace suna ci gaba don wayarwa da matasan Fulani kai, domin su daina zama suna sabawa doka da oda tare da fada musu muhimmancin zaman lafiya.

Saurari cikakken rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Shirin Samar Da Guraren Kiwo Ga Fulani Makiyaya A Najeriya - 2'57"