Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansandan Jihar Sokoto Sun Tarwatsa Shirin Auren Jinsi Daya


IBRAHIM K. IDRIS, babban sifeton 'yansandan Najeriya

Wasu da suka shirya daurawa maza biyu aure irin na 'yan luadi a Sokoto, hakansu bai cimma ruwa ba domin shirin ya kai kunnuwan 'yansandan jihar kuma sun yi masu diran mikiya.

'Yansanda sun samu nasarar kama mutane biyu a daidai lokacin da suke yunkurin daura auren tsakanin mazaje biyu a wani gidan haya dake Arkila a birnin Sokoto.

Wasu rahotanni da ba'a tantance ba sun ce mutanen sun zo ne daga Katsina tare da gayyar biki domin daura auren a Sokoto. Jama'ar unguwar ne suka ankara suka tseguntawa jami'an tsaro.

Kakakin rundunar 'yansandan Sokoto Sufritanda Al-Mustapha Sani ya tabbatar da aukuwar lamarin. Yace an tsegunta masu cewa za'a yi auren ranar 20 ga wannan watan. A adinanci da kuma dokar kasa duka basu amince da aure tsakanin jinsi daya ba.

Yace duk abun da ya sabawa addinin musulunci da dokar kasa dole ne su hana domin aikinsu ke nan.

Wadanda aka kama suna hannun 'yasandan kuma suna gudanar da bincikekafin su kai maganar kotu.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG