Shugaba CAF Ahmad Na Shirin Fafatawa Da Pinick Na Najeriya A Shugabancin CAF

Shugaban CAF Ahmad Ahmad.

Akwai yiwuwar shugaban hukumar kwallon kafar Afrika ta CAF Ahmad ka iya samun wa’adi na biyu, na jagorancin hukumar, yayin da kasashe 46 cikin 54 mambobin hukumar suka bukaci ya sake tsayawa takarar shugabancin hukumar.

Ahmad dan asalin kasar Madagsca wanda ya dauki ragamar shugabancin CAF a shekarar 2017, ya na samun goyon baya tun bai yanke shawarar sake shiga takarar zaben da za a yi a watan Maris 2021 ba.

Ranar 12 ga watan Nuwamba ce ranar karshe na shigar da takardun neman tsayawa takara ga duk mai neman yin takara.

Shugaan CAF Ahmad Ahmad

Wata sanarwa da shugabannin yan-kunan Afrika shida suka sanyawa hannu, na nuni da cewa dan shekaru 60 na samun goyon baya ainun, idan ya yanke shawarar shiga takara, koda yake maganar shi ce a tsakiyar batun da hukumar FIFA ke yi.

A baya Ahmad ya ce sai ya nemi shwarar daga masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa a nahiyar Afrika, kamun ya yanke shawarar shiga takara, yana mai cewa zai iya tsayawa saboda goyon bayan jama’a, amma ba dan bukatar kansa ba.

Shugaba Buhari Tare Da Kungiyar Kwallon Kafa Na Kasa Super Eagles

A watan da ya gabata, shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya Amaju Pinick, yaki janyewa daga neman shiga takara, inda yake cewa akwai abubuwa da dama da ba a yinsu dai-dai a hukumar ta CAF.