Shugaba Issouhou Ya Kori Babban Sojan Kasar

Shugaba Issouhou Mahamadou

A yayinda aka fara zaman makoki yau a jamhuriyar Nijar, biyo bayan mutuwar wasu sojojin kasar kusan 90, shugaba Issouhou Mahamadou ya sallami hafsan-hafsoshin sojin kasar Janar Ahmed Mohamed, da wasu mataimakansa daga mukamansu.

A taron majalisar ministocin da aka gudanar ne shugaban ya yanke shawarar aiwatar da sauye-sauyen mukamai a fannin tsaron kasar, bayan nazarin halin da ake ciki a ‘yan makwannin nan, da kimanin sojoji kusan 200 suka halaka cikin wata guda.

Janar Ahmed Mohamed Tsohon Kwamandan Rundunar Mayakan Jamhuriyar Nijar

A wata sanarwar da aka bayyanar a kafar rediyo, shugaba Issouhou Mahamadou ya nada Janar Salifou Mody, ya maye gurbin hafsan-hafsoshin sojin kasar ta Nijar Chef d’etat Major General des armees Ahmed Mohamed, yayin da Janar Seidou Bague ke daukar madafan rundunar mayakan kasa Chef d’Etat Major armee de terre.

Haka kuma gwamnatin ta sallami babban sufeton rundunonin mayaka wato Inspector General des armees da sakataren ma’aikatar tsaro daga mukamansu.

Lamarin da Nassirou Seidou na Voix des sans Voix ya ce zai yi tasiri a kokarin neman hanyoyin warware matsalolin da sha’anin tsaro ya shiga a wannan kasar.

Janar Salifou Mody Sabon Kwamandan Rundunonin Mayakan Jamhuriyar Nijar

Shugaba Issouhou, wanda a farko aka sanar cewa ba zai halarci taron G5 Sahel na Faransa ba, ya tashi a yau Litinin don zuwa birnin Pau inda ake gudanar da wannan taro.

Amma kafin nan, sai da ya ziyarci makarbartar Carre des Marthyrs dake Yamai inda ya rusunawa sojojin nan 89 da aka halaka a barikin Chinagoder ranar Alhamis din da ta gabata.

Ga karin bayani cikin sauti daga Nijar.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Issouhou Ya Kori Babban Sojan Kasar