Shugaban Kasar Turkiyya Ya Fara Ziyarar Aiki

Shugaban kasar Turkiya, Rajib Tayyip Erdowan, ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a babban birnin Somalia, a daidai lokacin da ake jimamin wani harin mayakan Al Shabab da ya kashe mutane da dama.

Wannan shi ne karo na uku da shugaban na Turkiyya ya ke kai ziyara a Mogadishu tun bayan wacce ya kai a watan Augustan shekarar 2011, ziyarar da ta ja hankulan duniya kan matsalar fari da kasar ke fama da ita a lokacin.

Shugaban Somalia, Hassan Sheikh Mahmud, ya tarbi Erdowan ne a filin tashin jiragen sama na Somalia a yau Juma’a.

Ayarin motocin shugaban na Turkiya, ya ratsa ta tsakiyar birnin unda ya nufi ofishin jakadancin kasar, wanda shugaba Erdowan zai kaddamar a hukumance a wannan ziyara tasa.

Shugaban na Turkiya, ya kai ziyarar ce duk da harin da mayaakn Al Shabab suka kai ranar Laraba a kan wani otel a Mogadishu, harin da ya yi sanadin mutuwar mutae 24, ciki har da maharan