Shugaba Obama Ya Soki Lamirin Rasha da Siriya Kan Hare-haren Aleppo

Shugaban Amurka Barack Obama

A daya bangaren kuma, shugaba Barack Obama ya yi kakkausar suka kan abinda ya kwatanta a matsayin “hare-haren rashin Imani” da dakarun Rasha da Syria ke kaiwa akan fararen hula a gabashin Aleppo.

Fadar White House ta ce Obama ya yi magana da Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta wayar talho a jiya Alhamis, inda shugabannin biyu suka amince cewa akwai “nauyi na musamman” da ya rataya a wuyan Rasha da gwamnatin Assad, dangane da ya yadda za a dakatar da yakin domin a shigar da kayayyakin jin kai.

Gabanin hakan, Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya ce Amurka na dab da dakatar da tattaunawar dimplomasiyya da Rasha saboda Moscow na ci gaba da yin ruwan bama-bamai a kan ‘yan tawaye a gabashin birnin na Aleppo.

Wata kungiya da ke sa ido akan rikicin na Syria a yau Juma’a ta ce hare-haren sama da Rasha ta kai a kasar, sun halaka sama da mutane dubu tara, cikin har da fararen hula.

Kungiyar mai suna Syrian Observatory for Human Rights da ke da hedkwata a Birtaniya, ta kuma kara da cewa an jikkta wasu fararen hula da dama.

Yanzu haka, daruruwan fararen hula na can makale a cikin birnin na Aleppo, kuma akasarinsu yara ne kanana.