Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya Laraba Aka Kai Hari Mafi Muni Akan Aleppo dake Siriya


 Bashar Al- Assad, shugaban Siriya
Bashar Al- Assad, shugaban Siriya

A daren jiya Laraba ne aka kai hare-haren jiragen sama ma fi muni a garin Aleppo, wannan harin shine mafi karfi da garin na Aleppo ya gani a wannan watan. Sa’o’i kadan bayan Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry yayi kira da a kawo karshen hare-haren na jiragen sama.

Tuni dai ‘Yan adawa suka zargi gwamnatin Syria akan wadannan hare-haren, duk da dai jami’an gwamnatin basu ce komai akai ba. Bayan wadannan hare-hare ne kuma kazamin fada ya barke a garin an Aleppo.

Harin Jiragen saman ya kashe kimanin fararen hula 12, wanda hakan ya janwo matsalar karya alkawarin tsagaita wutar
da Amurka da Rusha suka kulla a matsayin masu shiga tsakani tun a farkon wannan watan.

Kerry yace idan dai har ana son yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tangal-tangal ta dore, to lallai sai an dakatar da kai hare-hare da jiragen yaki. Musamman a wuraren da kungiyoyin agaji ke kokarin kai abinci da magunguna.

Kerry ya mika kukansa a babban taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya bayyana bukatar kayyade tashin jiragen yakin, da cewa yana da matukar muhimmanci don kawo karshe zubar da jini a Syria.

XS
SM
MD
LG