Shugaban Kamfanin Amazon Ya Zama Attajiri Mafi Kudi A Duniya

Shugaban Kamfanin Amazon, Jeff Bezos

Shugaban kamfanin sayar da kaya ta yanar wato Amazon.com, Jeff Bezos, ya zama attajiri mafi kudi a duniya wanda yake da zunzurutun kudi fiye da dala biliyon 105, a cewar mujallar tattalin arziki ta Bloomberg.

Yayin da kasuwar hannun jari take cirawa sama a kwannakin farko na wannan sabuwar shekarar ta 2018, arzikin Bezos yayi tashin goron zabi inda, a cikin kwannaki biyar kacal, dukiyarsa ta karu da Dala biliyon 6.

Masu nazarin harkokokin kudi sun sami sabanin ra’ayi akan ko Bezos shine mutum mafi kudi a duniya ko kuma watakila Bill Gates mai kamfanin Microsoft ne ya zarce kowa kudin.

Gates yana da arziki sama da Dala biliyon 90 amma masana harkar kudi sun ce da dukiyarsa zata fi hakan inda ba saboda yawan jinkai da taimakon da yake bayarwa a sassan duniya daban-daban ba.