Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Alibaba Ya Kusa Wargaza Kungiyar Yaki Da Kayan Jebu.


Babban ofishin kamfanin Alibaba a China.
Babban ofishin kamfanin Alibaba a China.

Kamfanoni da suka janye cikin kungiyar sun hada da Gucci, da Michael Koors, da Tiffany.

Wata kungiyar da take yaki da kayan jebu ta dakatar da katafen kamfanin nan na kasar China da ake kira Alibaba, wanda ya shahara wajen cinikayya ta internet, daga rukuninta, bayan da kamfanoni da suke kungiyar suka dare saboda kasancewar kamfanin na China a cikinsu, wanda suke kallon a zaman babba da ya fi ko wanne a duniya, zaman kasuwar kayayyaki na jebu.

A makonnin baya bayan nan dai kamfanin Gucci na Amurka, da Michael kors, da Tifany, sun fice daga kungiyar da take yaki da kayan jebu, saboda kasancewar Alibaba tsakaninsu.

Bugu da kari, kungiyar ta fito jiya jumma'a tana cewa, bata bayya nawa shugabannin kungiyar cewa akwai dangantaka tsakanin kamfanin Alibaba da shugaban kungiyar Robert Barchiesi.
Tun farko jiya jumma'a, kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya bada rahoton cewa, Barchiesi, ya sayi hanun jari a kamfanin Alibaba, kuma yana da dangantaka ta kud da kud da wani jigo na Alibaba, kuma ya sanya wani daga cikin danginsa yana tafiyar da ayyukan kungiyar.

Kungiyar tace zata dauki wani kamfani mai zaman kansa, ya sake nazarin manufofinta.

Jaridar Wall Street, ta ce kamfanin Alibaba a China ya tafiyar da cinikin kayayyaki na dala milyan dubu 485, a shekarar kudi data kare 31 ga watan Maris na bana. Wannan adadi masu fashin baki suka ce ya dara cinikayyar da kamfanonin Amazon, da Rbay baki daya.

Masu sukar lamirin Alibaba suka ce kayayyaki da Alibaba yake sayarwa jebu ne, wand a yake da kushe ribar kamfanoni da ake jebun kayyakinsu.

XS
SM
MD
LG