Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Da Tawagarsa Sun Isa Birnin Paris Na Kasar Faransa

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Da Tawagarsa Sun Isa Birnin Paris Na Kasar Faransa

Halartar shugaba Tinubu a wannan taro na nuni da kokarin Najeriya wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa da kuma neman habaka tattalin arzikinta. 

Shugaban da tawagarsa sun shirya tsaf don halartar babban taron na hada hadar kuɗaɗe da tattalin arziki na duniya (Global Financing Pact Summit), wanda shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa ya shirya.

Wannan babban taron koli ya hada shugabannin duniya da masana harkokin kudi daga ko'ina cikin duniya, da nufin magance muhimman kalubalen tattalin arziki da kulla kawance mai tasiri don samun ci gaba mai dorewa.

Halartar shugaba Tinubu a wannan taro na nuni da kokarin Najeriya wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa da kuma neman habaka tattalin arzikin ta.

~ Yusuf Aminu