Shugaban kasar Najeriya ya kaddamar da yakin neman zabe

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da yakin neman zabensa a garin Lafiya da ke a wani wuri mai muhimmanci.

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da yakin neman zabensa a garin Lafiya da ke a wani wuri mai muhimmanci. Dubban magoya bayan Mr. Jonathan sun halarci wani gangami a wannan karamin garin. An zabi Jonathan a matsayin dan takarar jam’iyya mai mulki duk ko da tsarin karba-karba tsakanin kudu da arewa. Jam'iyar PDP ke mulkin kasar tunda kasar ta koma mulkin damokaradiya cikin shekara ta dubu da dari tara da casa'in da tara.