Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gurfanar da Dillalan Makamai Gaban Shari'a a Nigeria


Azim Aghajani, an Iranian citizen, second right, and Nigerian Usman Abbas Jega, second left charged with orchestrating an illegal arms shipment into Nigeria are escorted at the Federal Hight Court in Lagos, Nigeria.

Dillalan Makaman nan biyu, dan kasar Iran da dan Nigeria, sun gurfana gaban shari’a a birnin ikkon Nigeria. An dauki tsauraran matakan tsaro a kotun da ake shari’ar ran laraba. Lauyan dake kare wadanda ake zargi Chris Uche ya bada hujjar cewa basu aikata laifin ba domin makaman suna kanhanyarsu c eta zuwa kasar Gambiya, zai kuna nuna muhimman takardun iznin shiga a lokacin daake gudanar da shari’a. Jakadan kasar Iran ya musanta cewar Iran tayi watsi da takunkumin da MDD ta aza mata.

An Gurfanar da Dillalan Makamai Gaban Shari'a a Nigeria

Jami’an Nigeria ne suka kame tulin makama a tashar jiragen ruwan Apapa dake birnin Ikon, kuma an kwaso makaman ne daga tashar jiragen ruwan Iran ta Banadar Abbas, aka rubuta cewar kayan gini ne. Lauyan wadanda ake yiwa shari’a Lauya Uche yana mai cewa babu wata niyya ta yin amfani ko ajiye wadannan makamai a Nigeria. Takardun shigada fitar da kaya daga jirgin ruwa sun tabbatar da cewar makaman suna kan hanyarsu ce ta zuwa kasar Gambiya, za’a kuma gabatarwa kotun da dukkan takardun da suka jibanci kaiwa da komowar wadannan makamai. Nigeria ta gabatar da kukanta gaban kwamatin sulhun MDD tana zargin kokarin da Iran keyi domin yin watsi da takunkumin da MDD ta azawa mata.Gwamnatin kasar Gambia tace ba abinda ya hadata da batun cinikayyar makamai da kasar Iran harma Gwamnatin Gambia ta katse huldar jakadanci da kasar Iran.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG