Shugaban Kasar Tunisia Beji Caid Essebsi Ya Rasu

Shugaban kasar Tunisia Beji Caid Essebsi, ya rasu yana da shekaru 92 da haihuwa.

Ofishin shugaban kasar Tunisia ya ce gwarzon dan siyasar ya rasu yau Alhamis, bayan da aka kai shi wani asibitin sojan kasar a daren ranar Laraba.

Dama an kwantar da shi asibiti a karshen watan da ya gabata, inda yake jinyar wani rashin lafiya mai tsanani.

Essebsi, shi ne shugaban kasa na farko da aka zaba a kasar a karkashin gwamnatin demokradiyya, kuma shine magajin wanda yayi gwagwarmayar kafa kasar, Habib Bourguiba, wanda ya gina kasar ya kuma ilmantar da al’ummar kasar.

Shi dai Essebsi, ya fara mulkin kasar ne a shekarar 2014, shekaru 3 bayan boren da aka yi a wasu kasashen larabawa wanda yayi sanadiyar hambarar da dadadden shugaban kasa, mai mulkin kama karya Zine El Abidine Ben Ali, ya kuma haddasa rikici a kasashen larabawa da yawa.