Shugabanin Musulmi Dana Kirista Sun Bukaci a Zauna Lafiya

Zaben 2015 a Najeriya. (File Photo)

Shugabanin addinin Musulunci da Kirista sun yi wani taron yin adu'o'in karfafa kumana lokacin zabe da kuma amincewa kadara.

Shugabanin addinin Musulunci dana Kirista sun yi wani taron karfafa lumana lokacin zabe da kuma amincewa kadara.

Sheikh Kabiru Haruna Gombe yace taron da suka yi, sara ne akan gaba. Sheikh Kabiru ya yi kira ga hukumar zabe data tsaya tayi zabe tsakanin da Allah ba tare da kaucewa ka'ida ba, bisa kuma dokokin da aka kafa.

Yace idan hukumar zabe ta yi haka, to ta taimaki zaman lafiya.

Shi kuma Reverend Hayab cewa yayi, matukar za'a dawo da zumunci tsakanin Musulmi da Kirista kamar da, to kuwa komai zai yi kyau

Reverend Hayap yace suna gudanar da irin wadannan tarurruka ne domin ganin an koma yadda ake ada. Aga Mallam yana hulda da Pasto. Aga matar Mallam tana hulda da matar Pasto. Hakazalika suma ya'yansu.

Shima Reverend Shua'ibu ya karfafa wannan matsayi.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugabanin Musulmi Dana Kirista Sun Bukaci a Zauna Lafiya - 2'59"