Shugabannin Rasha Da Turkiyya Da Iran Zasu Gana Kan Batun Lardin Idlib

Batun Siriya zai sake daukar hankali a fagen diflomasiyya a yau dinnan Jumma'a, inda jami'an diflomasiyya za su yi kokarin kau da yiwuwar zub da jini a lardin Idlib, yanki daya tilo da ya rage a hannun 'yan tawaye.

Shugabannin Rasha da Turkiyya da kuma Iran zu su yi wani taron koli a birnin Tehran kan batun.

Rasha da Iran kawayen Siriya ne na kud-da-kud kuma su na goyon bayanta ta fuskar soji, a yayin da kuma Turkiyya, wacce ke iyaka da Idlib, ta ke goyon bayan 'yan tawayen. Turkiyya na fargabar fuskantar matsalar 'yan gudun hijira muddun sojojin Siriya su ka kai harin.

A halin da ake ciki kuma, Kwamitin Sulhun MDD zai yi wani zama na gaggawa a birnin New York a yau jumma'a kan wannan batu na rikicin Syria.

"Daukar duk wani mataki na soji a Idlib ka iya jefa rayuwar mutane fiyeda milyan uku farar hula cikin hadari, ciki har da yara wajen miliyan daya da ke yankin," a cewar takardar bayanin.