Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Samar da zaman Lafiya a Afghanistan na Kankama


Janar James Mattis, skataren tsaron Amurka
Janar James Mattis, skataren tsaron Amurka

Sakataren harkokin tsaron Amurka Jim Mattis ne ya bayyana cewa kokarin da ake yi na maido da zaman lafiya a Afghanistan na samun ci gaba.

Yinkurin da ake yi na kawo karshen yakin shekaru 17 da Amurka ke jagoranta a Afghanistan na samun goyon baya, a cewar sakataren tsaro na Amurka, Jim Mattis.

Ko da yake ya ambaci “hanyar tattaunawa a bude ta ke,” Mattis bai fadi tattaunawar sharar fagen da rahotanni suka ce an yi tsakanin Amurka da ‘yan Taliban a Qatar ba. Idan hakan ya tabbata, to wannan ce za ta zama ganawar kai tsaye ta farko da Amurka ta yi da Taliban a cikin shekarun da suka gabata.

Haka kuma Mattis bai ce ko akwai wasu sabbin abubuwa da suka kai ga yin wannan nazarin ba. Amma duk da haka, ya ambaci yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 3 da ‘yan Taliban da gwamnatin Afghanistan suka ayyana a farkon shekarar nan.

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG