Sojojin Najeriya Sun Fattaki 'Yan Boko Haram

Dakarun Sojojin Najeriya.

Dakarun Sojojin Najeriya, na samun Nasarar fattakar mayakar kungiyar Boko Haram, a arewacin jihar Adamawa, inda suka kwato kusan dukka kananan hukumomin jihar dake hannun ‘yan kungiyar ta Boko Haram.

Dakarun Sojojin Najeriya, na samun Nasarar fattakar mayakar kungiyar Boko Haram, a arewacin jihar Adamawa, inda suka kwato kusan dukka kananan hukumomin jihar dake hannun ‘yan kungiyar ta Boko Haram.

Yayin da, jami’an hukumar bada agajin gaggawa a jihar ta Adamawa, suka leka wasu yankunan da aka kwato don tantance halin da ake ciki, kamar yadda babban sakataren hukumar Alhaji Hamman Foro, ya tabbatar.

Ya kara da cewa a cikin kananan hukumomi bakwai da aka kwato tabbas guda shida na hannun Gwamnatin jihar Adamawa, inda aka tura magunguna da kayan abinci domin tallafawa jama’ar, kananan hukumomin. Yace Gwamnati a shirye take domin ganin cewa jama’a sun koma gidajensu.

Rundunar Sojan Najeriya, dai ta sha alwashin kawarda mayakan, Boko Haram, a cikin makoni shida, wanda hakan ne yasa aka dage babban zabe, a Najeriya.

Kawo yanzu jiragen yaki ne ke cigaba da shawagi, yayin da a bangare guda Sojojin kasa na cigaba da sintiri domin tabbatar tsaron a yankunan.

Your browser doesn’t support HTML5

Dakarun Sojojin Najeriya - 3'03"