Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Ba’a Makonni 6 Za’a Kori Boko Haram Ba – inji Namadi


Muryar Amurka ya samu damar tattauna da mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Namadi Sambo. Ibrahim Alfa Ahmed na Sashen Hausa ya tattauna batutuwa masu nasaba da tsaro da Mr. Sambo, da ma zabe mai zuwa.

“Insha Allahu, na tabbata (jami’an tsaro) zasu yi iyakacin kokarinsu su tabbatar da cewa an samu yanayin da za’a iya yin zabe a kasarnan” a cewar mataimakin shugaban.

Namadi Sambo ya cigaba da cewa “su kuma INEC, ina kyautata zaton zasu yi amfani da wannan damar su ga cewa, an baiwa kowa katin da zai je, yayi zabennan.”

Game da batun tsaro kuwa, yawanci abunda mutane suke tunawa shine batun Boko Haram da ake fama da shi musamman a arewacin Najeriya. Shin za’a iya cin galaba akan Boko Haram a cikin wannan lokaci da aka dauka har aka dage zabe?

Mr. Sambo yace “inda ake samun kuskure gane abunda su masu tsaron kasa sukeyi, ba wai suna bayanin cewa a cikin sati shida za’a kori duk Boko Haram ne ba, a’a. Amma cikin sati shida, (jami’an tsaro) zasu kawo yanayin da zasu iya bada nasu gudunmuwa na tabbatar da cewa an samu isasshen tsaro a duk Najeriya, yanda ko ina za’a iya yin zabe.”

A halin yanzu jama’ar Najeriya na jiran babban zabe dake tafe nan da makonni 6, wanda da ranar 14 ga watannan na Fabrairu za’a fara, amma aka jinkirta shi saboda dalilai na tsaro. Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan wanda yake yakin neman komawa kan karagar mulki na shan suka wajen masu kalubalantar gwamnatinsa, musamman wajen tabbatar da tsaro a kasar dake yammacin Afirka.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG