Sojojin Najeriya Sun Hallaka Maharan IPOB Hudu A Jihar Anambra

'Yan Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra (IPOB)

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun ta sun hallaka wasu ‘yan awaren kungiyar IPOB da ke fafutukar kafa kasar Biafra guda hudu a karamar hukumar Ihiala da ke jihar Anambra, yayin da suka yi kokarin tilasta wa jama’a zaman gida a ranar Litinin da ta gabata.

Rundunar sojin kasar ta bayyana hakan ne a wata sanarwar da ta fitar ranar Laraba ta hannun kakakin ta Birgediya Janar Onyema Nwachukwu.

Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar soji ta shiyya 82 da ke Inugu, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu sanarwar ‘yan aware sun bude wuta a wani gidan mai da ke wajen garin Ihiala ne, shi ya sa jami’an tsaro zuwa wurin.

Ku Duba Wannan Ma 'Yan Awaren Biafra Na Kara Tilasta Dokar Zaman Gida Kan Shari'ar Nnamdi Kanu

Ya kuma ce jami’an tsaron sun kashe hudu daga cikin ‘yan awaren a musayar wutar da ta auku a lokacin da maharan suka yi kokarin shiga garin don tursasawa jama’a zaman gida, sai dai jami’an tsaro biyu sun rasa rayukansu sakamakon arangamar yayin da wasu biyu kuma suka jikkata. Bayan haka jami’an tsaro sun iya kwato makamai daga hannun ‘yan awaren.

Karamar hukumar Ihiala dai na daya daga cikin wuraren da hare haren ‘yan bindiga da ayyukan ‘yan awaren Biafra suka fi yawaita a yankin kudu maso gabashin kasar, kuma rundunar sojin Najeriya ta ce ta na ci gaba da bada gudummowa wajen inganta tsaro a wannan karamar hukumar da ma kewayenta.

Saurari cikakken rahoton Alphonsus Okoroigwe.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Najeriya Sun Hallaka Maharan IPOB Hudu A Jihar Anambra